Acts 10

Korneliyus Ya Kira Bitrus

1A Kaisariya akwai wani mutum mai suna Korneliyus, wani jarumin Roma ne, a ƙungiyar soja da ake kira Bataliyar Italiya. 2Shi da dukan iyalinsa masu ibada ne masu tsoron Allah kuma; yakan ba da kyauta hannu sake ga masu bukata yana kuma adduʼa ga Allah ba fasawa. 3Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma ya ga wahayi. A sarari ya ga wani malaʼikan Allah, wanda ya zo wajensa ya ce, “Korneliyus!”

4Korneliyus kuwa ya zura masa ido a tsorace ya ce, “Mene ne, ya Ubangiji?”

Malaʼikan ya ce, “Adduʼoʼinka da kyautayinka ga matalauta sun kai har sama, hadayar tunawa ce a gaban Allah.
5Yanzu sai ka aiki mutane zuwa Yoffa su dawo da wani mutum mai suna Siman wanda ake kira Bitrus. 6Yana zama tare da Siman, mai aikin fatu, wanda gidansa ke bakin teku.”

7Saʼad da malaʼikan da ya yi masa magana ya tafi, sai Korneliyus ya kira biyu daga cikin bayinsa da kuma wani soja mai ibada wanda yake ɗaya a cikin masu yin masa hidima. 8Ya fada musu duk abin da ya faru saʼan nan ya aike su Yoffa.

Wahayin Bitrus

9Wajen tsakar rana washegari yayinda suke cikin tafiyarsu suna kuma dab da birnin, sai Bitrus ya hau bisan rufin gida yǎ yi adduʼa. 10Yunwa ta kama shi ya kuwa so yǎ ci wani abu, yayinda ake shirya abinci, sai wahayi ya zo masa. 11Ya ga sama ya buɗe ana kuwa saukowa wani abu ƙasa kamar babban mayafi zuwa duniya ta kusurwansa huɗu. 12Cikinsa kuwa akwai kowace irin dabba mai ƙafa huɗu da masu jan da ciki na duniya da kuma tsuntsayen sararin sama. 13Saʼan nan wata murya ta ce masa, “Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.”

14Bitrus ya ce, “Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.”

15Muryar ta yi magana da shi sau na biyu ta ce, “Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.”

16Wannan ya faru har sau uku, sai nan da nan aka ɗauke mayafin zuwa sama.

17Tun Bitrus yana cikin tunani game da maʼanar wahayin nan, sai ga mutanen da Korneliyus ya aika sun sami gidan Siman suna kuma tsaye a ƙofar. 18Suka yi sallama, suna tambaya ko Siman wanda aka sani da suna Bitrus yana zama a can.

19Yayinda Bitrus yana cikin tunani game da wahayin, sai Ruhu ya ce masa, “Siman, ga mutum uku suna nemanka. 20Saboda haka ka tashi ka sauka. Kada ka yi wata wata, gama ni ne na aiko su.”

21Sai Bitrus ya sauka ya ce wa mutanen, “Ni ne kuke nema. Me ya kawo ku?”

22Mutanen suka amsa, “Mun zo ne daga wurin Korneliyus wani jarumin. Shi mutum ne mai adalci mai tsoron Allah kuma, wanda dukan Yahudawa ke girmamawa. Wani malaʼika mai tsarki ya faɗa masa, yǎ sa ka zo gidansa don ya ji abin da za ka faɗa.” 23Sai Bitrus ya gayyaci mutanen cikin gida su zama baƙinsa.

Bitrus a Gidan Korneliyus

Washegari Bitrus ya tafi tare da su, waɗansu ʼyanʼuwa daga Yoffa kuwa suka tafi tare da shi.
24Washegari sai ya iso Kaisariya. Korneliyus kuwa yana nan yana jiransu, ya kuma gayyaci ʼyanʼuwansa da abokansa na kusa. 25Da Bitrus ya shiga gidan, Korneliyus ya sadu da shi ya kuma fāɗi a gabansa cikin ban girma. 26Amma Bitrus ya sa shi ya tashi. Ya ce, “Tashi, ni mutum ne kawai.”

27Yana magana da shi, sai Bitrus ya shiga ciki ya kuma tarar da taron mutane da yawa. 28Sai ya ce musu: “Ku da kanku kun san cewa dokarmu ta hana Bayahude yin cuɗanya, ko ya ziyarci Baʼalʼumme. Amma Allah ya nuna mini cewa kada in kira wani mutum marar tsarki ko marar tsabta. 29Don haka saʼad da aka aika in zo, na zo ba wata faɗa. To, ko zan san abin da ya sa ka aika in zo?”

30Korneliyus ya amsa, ya ce: “Kwana huɗu da suka wuce ina a gidana ina adduʼa a wannan lokaci, wajen ƙarfe uku na yamma. Ba zato ba tsammani sai ga wani mutum cikin tufafi masu walƙiya ya tsaya a gabana 31ya ce, ‘Korneliyus, Allah ya ji adduʼarka, ya kuma tuna da kyautayinka ga matalauta. 32Ka aika zuwa Yoffa don a kira Siman wanda ake ce da shi Bitrus. Shi baƙo ne a gidan Siman mai aikin fatu, wanda yake zama a bakin teku.’ 33Saboda haka na aika a zo da kai nan da nan, ya kuma yi kyau da ka zo. To ga mu duka a nan a gaban Allah don mu saurari dukan abin da Ubangiji ya umarce ka ka faɗa mana.”

34Saʼan nan Bitrus ya fara magana ya ce: “Yanzu na gane yadda gaskiya ne cewa Allah ba ya sonkai 35amma yana karɓan mutane daga kowace alʼummar da take tsoronsa suke kuma aikata abin da yake daidai. 36Kun san saƙon da Allah ya aika wa mutanen Israʼila, yana shelar labari mai daɗi na salama ta wurin Yesu Kiristi, shi ne kuwa Ubangijin kowa. 37Kun san abin da ya faru a dukan Yahudiya, farawa daga Galili bayan baftismar da Yohanna ya yi waʼazi—  38yadda Allah ya shafe Yesu Banazare da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da kuma yadda ya zaga koʼina yana aikata alheri yana kuma warkar da dukan waɗanda suke ƙarƙashin ikon Iblis, domin Allah yana tare da shi.

39“Mu kuwa shaidu ne na dukan abin da ya yi a ƙasar Yahudawa da kuma a Urushalima. Suka kashe shi ta wurin rataye shi a kan itace, 40amma Allah ya tashe shi daga matattu a rana ta uku, ya sa kuma aka gan shi. 41Ba dukan mutane ne suka gan shi ba, amma ta wurin shaidun da Allah ya riga ya zaɓa— ta wurin mu da muka ci muka kuma sha tare da shi bayan tashinsa daga matattu. 42Ya umarce mu mu yi waʼazi ga mutane mu kuma shaida cewa shi ne wanda Allah ya naɗa yǎ zama mai shariʼa na masu rai da na matattu. 43Duk annabawa sun yi shaida game da shi cewa duk wanda ya ba da gaskiya gare shi zai sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.”

44Tun Bitrus yana cikin faɗin waɗannan kalmomi, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka wa duk waɗanda suka ji saƙon. 45Masu bin da suke da kaciya waɗanda suka zo tare da Bitrus suka yi mamaki cewa a ba da kyautar Ruhu Mai Tsarki har ma a kan Alʼummai. 46Gama sun ji su suna magana da waɗansu harsuna suna kuma yabon Allah.

Sai Bitrus ya ce,
47“Wani zai iya hana a yi wa waɗannan mutane baftisma da ruwa? Sun karɓi Ruhu Mai Tsarki kamar yadda muka karɓa.” 48Saboda haka ya ba da umarni a yi musu baftisma cikin sunan Yesu Kiristi. Saʼan nan suka roƙi Bitrus yǎ zauna da su na ʼyan kwanaki.

Copyright information for HauSRK